Alanguburo yafadawa sheyi: Shishshiginka yayi yawa Kabarni Nayi Aikina Tunda Ba kaine kanaɗa Ni a matsayin Mataimakin shugaban ƙasa Ba, Shettima Ya Koka Kan Yunkurin Karbe iko daga Hannunsa Wanda Sheyi Tinubu yake ƙoƙarin yi a Halin yanzu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana damuwarsa kan abin da ya kira yunkurin kwace aikinsa, yana zargin dan Shugaba Bola Tinubu da yin ayyukan da ya kamata ya gudanar.
Shettima ya ce Ban taɓa jin kaina a matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa ba. Duk da cewa ya kamata in gudanar da muhimman ayyuka, dan Tinubu ne yake yin aikina.”
Ya kuma nuna damuwa kan yadda ake nuna wariya ga yankin Arewa, yana mai cewa an rage masa iko a matsayinsa na na biyu a ƙasar. Ya ce:
“Na taɓa tunanin yin murabus daga matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa sau da dama domin duniya ta ga hakikanin halin Tinubu. Sanya ni a wannan matsayi domin kawai a riƙe Arewa yayin da danka yake yin aikina, ba komai bane face iz@gili.”
- Menene ra’ayinku game da wannan batu?