RUNDUNAR YAN SANDAR JAHAR KANO TAYI BABBAN KAMU INDA TA KAMA MANYAN MASU AIKATA LAIFUKA DABAN DABAN
Rundunar Yan sanda jihar Kano ta kama mutane 78 tare da kwato manyan kadarori
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane 78 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a fadin jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ibrahim Bakori, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Bompai Kano, ya ce an kwato kayayyaki daban-daban da suka hada da bindigogi, muggan makamai, miyagun kwayoyi, da kadarori na sata daga hannun wadanda ake zargin.
CP Bakori ya bayyana cewa sun kwato motoci takwas (8) da kudin Dalar Amurka dari da casa’in da takwas (198) da kuma kudin jabu na naira dubu dari uku da goma sha daya (N311,000:00).
Shugaban rundunar ‘yan sandan Kano ya kuma sanar da kama wani fitaccen mai sayar da muggan kwayoyi, Sulaiman Danwawu da ke unguwar Tudun Yola Quarters Kano, tare da kwato manyan muggan kwayoyi.
“Wanda ake zargin ya shahara wajen dillancin miyagun kwayoyi, rundunar ‘yan sanda ta kama shi a ranar 31 ga Yuli, 2022, tare da kwalaye 500 na allunan Tramadol guda 500 kuma an gurfanar da shi a gaban kotu amman duk da haka bai tuba ba.
“Hakazalika, bayan bayanan sirri, an kama wani da ake zargin dan fashi da makami ne tare da kwato bindigogin Beretta guda biyu (2) tare da harsashi guda goma (10).”
Daga cikin wadanda aka kama akwai mutane biyar da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, da dillalan miyagun kwayoyi guda bakwai, daya da ake zargin barayin shanu ne, da ‘yan damfara hudu, da barayi goma sha uku, da kuma ‘yan daba guda arba’in da takwas (Yan Daba).
CP Bakori ya bayyana cewa an samu nasarorin da aka samu ta hanyar daukar matakan rigakafin zaman lafiya domin rage yawan laifuka zuwa kanana.
“Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tsara dabarun yaki da miyagun laifuka ta hanyar kara sanya ido a guraren Al’umma da sintiri ba dare ba rana, da amsa kiraye-kirayen da suka dace, da ayyukan tsaro tare da hadin gwiwa da kananan hukumomi.
Ya kuma ba da tabbacin rundunar ta jajirce wajen ganin an ci gaba da samun zaman lafiya ,
A FADIN JAHAR GABA DAYA
ALLAH YABAMU ZAMAN LAFIYA A NIJERIYA GABAKI DAYA
AMEN