LABARI DADUMI DUMINSA IRAN 🇮🇷 TA AIKATA MUMMUNAN HARI KAN ISRAEL 🇮🇱
YANZU-YANZU (19 Yuni, 2025): Rahotanni sun tabbatar da cewa Iran ta kai hari kai tsaye kan Cibiyar Saka Hannun Jari ta Isra’ila da ake kira Diamond Exchange District da ke Ramat Gan, kusa da Tel Aviv.
Iran ta harba makamai masu linzami kai tsaye zuwa Diamond Exchange District, wata cibiyar kasuwanci da ke da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Isra’ila.
Wasu daga cikin ginin Tel Aviv Stock Exchange sun samu lahani.
Har ila yau, wasu hare-hare sun shafi Soroka Medical Center da wasu yankuna a Be’er Sheva da Tel Aviv.
Muhimmancin Diamond Exchange District:
Wannan wuri na dauke da manyan gine-ginen kasuwanci da suka hada da gine-ginen hada-hadar lu’u-lu’u, bankuna, da ofisoshin saka hannun jari.
Yana daga cikin cibiyoyin kasuwanci mafi girma a Gabas ta Tsakiya.
An ruwaito cewa wasu gine-gine sun sami mummunan rauni.
A cewar hukumomin lafiya, an samu mutane da dama da suka jikkata, amma ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba tukuna.
Majalisar Dinkin Duniya da ƙasashe irin su Amurka da Faransa na kira da a dakatar da daukar fansa da sake tunani kan tasirin wannan rikici.
BANYAN SHUGABAN AMERICA DOLAN TRUMPÂ YAYIWA IRAN BARAZANAR KAIMUSU MUGGUN HARE HARE AKAN IDAN BASU TSAGAITA HUTABA WANNAN KALAMAN SUN HAR ZIKA KASAR IRAN DIN ADARAN JIYA SUKAKAI HARE HARE AKAN CHIBIYAR HADA HADAR JARI DA BUNKASA TATTALIN ARZIKI