LABARIN WASANNI
Arsenal da Tottenham na gogayya kan Eze, Spurs ta yi wa Romero farashi, United ta sake komawa kan maganar Gyökeres, Napoli da Juventus na son Sancho, United ta shiga zawarcin Zaire-Emery, Leicester City ta raba gari da Ruud Van Nistelrooy
Arsenal za ta yi gogayya da Tottenham wajen ɗaukan ɗanwasan Crystal Palace da Ingila Eberechi Eze mai shekara 26 wanda aka yi wa farashi fam miliyan 68. (Sun)
Arsenal na ƙyalla ido kan Eze wanda farashinsa bai kai ɗaya zaɓinta ba na ɗanwasan Real Madrid Rodrygo mai shekara 24. (Talksport, external)
Tottenham ta ƙiyasta farashin Cristian Romero mai shekara 27 kan sama da fam miliyan 60 kuma ba su shirya cefanar wa Atletico Madrid shi ba kan farashi mai sauƙi. (Telegraph – subscription required)
Napoli da Juventus na shirin biyan Manchester United fam miliyan 25 kan Jadon Sancho mai shekara 25 amma ba za ta iya biyan fam miliyan dubu 250 kowane mako ba ga ɗanwasan. (Metro)
Manchester United na duba yiwuwar sayen ɗanwasan Paris St-Germain da Faransa Warren Zaire-Emery mai shekara 19. (Teamtalk)
Fulham ba ta da sha’awar cefanar da ɗanwasanta Rodrigo Muniz mai shekara 24 duk da cewa Leeds ta nuna sha’awar sayen ɗanwasan. (Sky Sports)
Liverpool ta soma tattaunawa da Crystal Palace kan yarjejeniyar sayen kyaftinsu Marc Guehi inda bayanai ke nuna cewa ɗanwasan mai shekara 24 ya fi sha’awar komawa Anfield a bazara. (Teamtalk, external)
Newcastle ta fara zawarcin ɗanwasan Brighton mai shekara 23 Joao Pedro da golan Burnley James Trafford mai shekara 22 da kuma Anthony Elanga mai shekara 23 da ke bugawa Nottingham Forest. (Telegraph – subscription required)
Trafford ta amince da ƙa’idojin Newcastle sannan ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ƙungiyoyin biyu. (Fabrizio Romano)
Manchester United ta ƙara komawa kan batun sayen ɗanwasan Sporting Victor Gyokeres yayin da bayanai ke cewa ɗanwasan mai shekara 27 ke nuna cewa a shirye yake ya sake haɗuwa da tsohon kocinsa Ruben Amorim a Old Trafford. (Mirror, external)
West Ham na fafatawa da Wolves a sayen ɗanwasan Nice da Ivory Coast Evann Guessand mai shekara 23 da darajarsa ta kai fam miliyan 25. (Mail)
Brentford ta amince da yarjejeniyar sayen ɗanwasan Feyenoord mai shekara 20 Antoni Milambo wanda ɗanwasan Netherlands ne a matakin ƴan ƙasa da shekara 21. (Mirror)
Leicester City ta raba gari da Ruud Van Nistelrooy a matsayin mai horas da ƙungiyar.
Manchester United ta chigaba da bibiyar dan wasan sporting pc vector Gyökeres aljazirahausa.com.ng