GAMAIYAR JAMI,EN TSORO SOJA DA POLICE DA YAN BANGA SUNA HALAKA masu garkuwa da mutane da dama achiki harda kanin bello turji kuma babban kwamandansa
An Hallaka Babban Ɗan Uwan Turji Kuma Babban Yaronsa Yalo Ɗanbokolo a Ƙaramar Hukumar Shinkafi.
Ɗanbokolo, ɗan uwa ne ga shahararren ɗan bindiga Bello Turji, ya mutu bayan samun wata luguden wuta da harbin bindiga a wata arangama mai zafi dashi da Jami’an tsaron gari.
Majiyoyin tsaro sun shaida wa AIT News cewa akalla mayakansa 173 sun mutu a wannan hari wanda mazauna yankin suka bayyana a matsayin “babbar nasara da ba’ayi tsammani nan kusa ba”, kuma shi ne mafi munin hari a tarihin yaƙi da ƴan bindiga a wannan yanki.
Duk da cewa Hukumar Tsaro ta DSS ba ta tabbatar da rawar da ta taka ba, wasu majiyoyi sun ce hukumar ta bayar da goyon bayan sirri a harin.
A gundumar Kurya da wasu ƙauyuka da ke makwabtaka da ita, al’umma sun fara murna da shagulgula da jin labarin kisan, Manoma da mazauna yankin na murnar kawo ƙarshen zaman fargaba, haraji da hare-haren kisan gilla da suka dade suna fuskanta.
Danbokolo, wanda ake ɗauka a matsayin gwarzon jagoran ayyukan ta’addanci a Arewa maso Yamma, ana ganin shi ne ke tsara hare-hare, yayin da Turji ke matsayin mai magana da yawun su,
Mazauna yankin sun ce magoya bayan Turji sun shiga ruɗani, tare da rahotanni da ke nuna cewa wasu daga cikinsu na neman afuwa yayin da rundunonin tsaro ke ƙara matsa lamba., Wannan shi ne karon farko da ƴan bijilanti suka kai hari kai tsaye kan sansanin Turji tun bayan da ta’addanci ya mamaye yankin.
Al’umma sun bayyana fatan su na samun damina ta noma da za ta kasance babu haraji ko tsoro, tare da nuna godiya ga gwamnatoci kan bayarda goyon baya a yaki da ta’addanci Mutuwar Danbokolo na iya zama babban ci gaba a yaƙin da ake yi da ta’addanci a Arewa maso Yamma gwamnatin jahar zamfara ta jinjinawa yan banga kan wannan lamari
GWAMNATIN TARAYYA TABAWA SOJOJI UMARNI KAN KAWO KARSHAN YAN, TA,ADDA⁹