Wasu gwamnoni na jam’iyyar adawa guda biyar nashirin komawa APC me mulki

WASU GWAMNONI BIYAR NA JAM.IYAR ADAWA NASHIRIN KOMAWA APC ME MULKI

Gwamnonin Bayelsa, Rivers, Plateau, Kano da Wasu na Dab da Koma wa APC — Inji Jigon Jam’iyyar

Abuja, Najeriya — Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na sa ran karɓar sabbin gwamnonin jihohi da dama daga jam’iyyun adawa cikin watanni biyu masu zuwa, in ji Mataimakin Shugaban APC na Kudu maso Gabas, Dakta Ijeoma Arodiogbu.

A wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Lahadi, Dakta Arodiogbu ya bayyana cewa wannan sauyin sheƙa ba zato ba tsammani ba ne, domin tuni tattaunawa da shirye-shiryen da suka dace sun kankama tsakanin bangarorin da abin ya shafa.

“Muna magana ne kan gwamnonin jihohin Bayelsa, Rivers, Plateau, Kano, da ɗaya daga cikin Abia ko Enugu. A cikin watanni biyu masu zuwa, za ku ga su na shigowa jam’iyyar APC a hukumance,” in ji shi.

Ya bayyana cewa shirye-shiryen da wasu ‘yan siyasa ke yi na kafa wata haɗakar jam’iyyun adawa wata dabara ce ta jan hankali a kafafen yaɗa labarai, ba wani yunkuri na gaske ba.

“Wannan magana ta haɗa jam’iyyun adawa tamkar wasan kwaikwayo ne kawai da ake yi domin su ci gaba da kasancewa cikin kanun labarai. Amma gaskiya ita ce, ’yan Najeriya na biye da jam’iyya da ke ba da aiki da sauyi, wato APC,” in ji Arodiogbu.

Da yake amsa tambaya kan makomar Gwamna Douye Diri na Bayelsa da Gwamna Ademola Adeleke na Osun, Arodiogbu ya ce Bayelsa na cikin gwamnatocin da ke yin shiri na sauya sheƙa.

“Na ambaci Bayelsa ne saboda akwai alamun hakan. Amma dangane da Adeleke, ba zan iya tabbatarwa da cikakken bayani ba, ko da yake na san yana yunkuri.”

Ya kuma ƙara da cewa suna lura da yiwuwar shigowar Gwamna Alex Otti na Abia da Gwamnan Jihar Enugu cikin jam’iyyar ta APC nan ba da jimawa ba.

WANNA NABIYO BANYAN  NADA SABON SHUGABAN JAM.IYAR APC

Aljazirahausa.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *