OMOYELE SOWARE NASAN TSAYAWA NEMAN TAKARAR SHUGABAN KASA NNAJERIYA A 2027
Ban yi tarayya da Bola Ahmed Tinubu wajen sayar da hodar Iblis a Chicago ba.
Ban yi tarayya da @Atiku Atiku Abubakar wajen wawusar dukiyar Hukumar Kwatsam ta Nijeriya ba.
Ban yi tarayya da David Mark ba, lokacin da ya karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin warware matsalar wayar tarho wanda daga baya ya taimaka wurin murƙushe fatan da muke da shi na demokradiyya a ranar June 12.
Ban yi tarayya da Abubakar Malami SAN wajen take hakkin bil’adama ba tare suburbuɗan dukiyar jama’a ƙarƙashin Muhammad Buhari, wanda ya haɗa da haramta @Twitter
Ban yi tarayya da Nasir El-Rufai @elrufai wajen kisan kiyashi akan ‘Yan Shia ba, da kuma rura rikicin kisan ƙare-dangi a Kudancin Kaduna. Ban yi tarayya da @PeterObi a tashar ruwa na Tin Can Ports ba lokacin da ya ringa taimaka wa Sani Abacha wurin shiga da fitan kayayyakinsa yayin da ƙasar take ta rugujewa ɗaya bayan ɗaya.
Ban yi tarayya da Sule Lamido ba, wanda tare maciya amanar jam’iyyar SDP suka sayar da kujerar MKO Abiola da kuma zaɓin al’ummar Nijeriya lokacin gwagwarmayar June 12.
Ban yi tarayya da @ChibuikeRotimi1 Chibuike Rotimi Amaechi ba lokacin da ya yi watsi Jihar Rivers ta hanyar barin aikin karamin hanyar jirgin ƙasa bayan an gama biyan kuɗin.
Ban taɓa shiga ko sa kaina cikin ɓarayi ba. Ban taɓa rusunawa ga duk wata kungiyar harigido ba ko da tana da farin jini, ƙarfi ko ƙarbuwa.
Abu ɗaya nake rusana masa: shi ne abin da ya shafi waɗanda aka zalunta, da waɗanda aka hana su zaɓe, da waɗanda aka musu duka kuma aka hana su kuka.
Zan yi tarayya ne ƙadai da waɗanda suke shirye su kawo ƙarshen wannan masifa da ta shafi ƙasarmu waɗanda waɗannan gungun mutane da na ambata suka sa mu a ciki.
Ina shelar cewa: ina tare da rundunar tabbatar da adalci. Gamayyar gaskiya. Mutane masu ra’ayin kawo juyin-juya-hali domin dawo da martabar mutanen Nijeriya da Afirka baki ɗaya.
Dole a ceto Nijeriya daga waɗanda shaiɗanu!
da alamu za akai ruwa rana a zaben shugaban kasa 2027 a Najeriya duba da siyasar nata kara yamutsa hazo