Anata fafatawa tsakanin Manchester United da Brentford akan danwasan
Gaba na Brentford Mbuemo
Shin kunsan menene ya hana kammala cinikin mbuemo sati 3 daya wuce?
Amsa
Manchester United ta mika tayin farko na £45+10 add-ons Wanda Brentford taki amincewa daga Baya united ta sake komawa da £55+7.5 add-ons Brentford ta tabbatar musu da suna bukatar £70m ne
Makusanta Brentford sun Fara shirin bankwana da mbuemo don suna ganin kamar cinikin ya kammala
Brentford tayi duba da irin kudin da aka zayi João Pedro da elanga Wanda suna ganin mbuemo yafisu
Wannan dalilin yasan Brentford suka chanja shawara daga 65m zuwa 70m Amma a farko sunce sunaso united ta biya daidai kudin da suka biya a Cunha Amma yazama instalments din farko yazama 50%
Sir Jim shine ya dakatar da Wilcox daga tattaunawar inda yace ba haka sukayi da Brentford ba
A yanzu united din takoma da sabuwar magana Wanda suna ganin shine zai iya Basu mbuemo Kai tsaye
Wilcox na son mbuemo a united kafin ranar talata tafiyar su zuwa American tour
Shin wani lokaci kuke hasashen wannan cakwakiyar zata kare
Kokuma United din idan kura takai bango zasu iya hakura da dan wasan amma dai lokachi yana kokarin kurewa shin menene fatan ku gama da Manchester United din