Gwamnatin jihar Kano tasiyo manya motochin shara

Gwamnatin jihar Kano tasiyo manya motochin shara na million kudade

Ɗaya Daga Cikin Motocin da Aka Sayi Ƙarƙashin Shirin ACReSAL Ya Isa Kano Shaidar Aiki Mai Gaskiya a Zamanin Dr. Dahir M. Hashim

Al’hamdulillah, Ɗaya daga cikin motocin da aka siya ƙarƙashin babban shirin raya muhalli da gina juriya ga sauyin yanayi Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL) yanzu haka ya isa jihar Kano, kuma hakan wata babbar shaida ce ta yadda Dr. Dahir M. Hashim, tsohon shugaban ACReSAL a jihar Kano, ya gudanar da aikinsa da gaskiya, kishi, da hangen nesa.

Motar, wacce aka siyo ta ne domin sauƙaƙa aikace-aikacen kimiyya da fasaha a fannoni kamar:
• Kula da muhalli,
• Inganta noman zamani,
• Da dakile illa da sauyin yanayi a karkara da birane,

…ta kasance wani babban ci gaba da aka samu daga hadin gwiwar Bankin Duniya (World Bank), Gwamnatin Tarayya da kuma Gwamnatocin Jihohi.

• Zirga-zirgar ma’aikata zuwa wuraren da ke fama da fari, sare dazuka, da ambaliya.
• Isar da kayan aiki da injuna zuwa gonaki da cibiyoyin bincike na noma.
• Sauƙaƙe isowar kayan aikin fasaha zuwa ƙauyuka masu nisa da wahalar isa.
• Ƙarfafa saurin aikin gyaran kasa, dasa bishiyoyi, da aikin shan ruwa.

Wannan mota daya daga cikin kayayyakin da aka siya a zamanin Dr. Dahir M. Hashim, ya zama abun koyi da wakilci na shugabanci nagari. Har yanzu, ana ci gaba da amfana da tsare-tsaren da ya shimfiɗa a lokacin shugabancinsa a ACReSAL.

“Aiki yana magana da kansa”, kamar yadda jama’a suka bayyana. Wannan mota wani tubali ne daga cikin ginin cigaba mai dorewa da aka kafa.

ALLAH ya saka da alheri ga duk waɗanda suka taka rawa a wannan aiki. Muna rokon Allah ya ba mu shugabannin da za su dora daga inda na gari suka tsaya masu kishi, nagarta, da amana.

Allah kasa mudace amen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *