HAYHUWAR YA,YA DAYAWA MATSALACE A WANNAN ZAMANIN
SHEKARA 40 Da Suka Wuce kowa Yana Kwadayin Ya Tara ‘Ya’ya. Amma Yanzu Mutane Tsoron Tara ‘Ya’ya Sukeji.
……………………………………
SHEKARA 40 Da Suka Wuce ‘Ya’ya ke Yiwa Iyaye Biyayya. Yanzu Iyaye Ke Yiwa ‘Ya’ya Biyayya.
………………………………….
SHEKARA 40 Da Suka Wuce Aure Nada Sauki Sakin Mace Keda Wuya. Yanzu Aurene Da Wuya Sakin Macene Da Sauki.
………………………………….
SHEKARA 40 Da Suka Wuce Duk Munsan ‘yan Unguwarmu. Yanzu Dan Unguwarku Kakewa Kallon Bako.
…………………………………..
SHEKARA 40 Da Suka Wuce Har Musun Fifikon Shekaru Mukeyi. Yanzu Kowa So Yake A Rage Masa Yawan Shekaru.
………………………………….
SHEKARA 40 Da Suka Wuce Har Gasar Fifikon Qiba Muke Yi. Yanzu Kowa Gudun Qiba Yake Saboda A Burge.
………………………………….
SHEKARA 40 Da Suka Wuce Attajirai ke Qoqarin Nuna Suma Talakawane. Yanzu Talakawa ke Qoqarin Nuna Suma Attajirai Ne.
……………………………………
SHEKARA 40 Da Suka Wuce Mutum Daya ke Nema Kuma Ya Dauki Nauyin Gidan Gaba Daya. Yanzu Duk Gidan ke Aiki Dan Adauki Nauyi Yaro Daya.
………………………………….
SHEKARU 40 Da Suka Wuce Mutane ke Zaman Jiran Lokacin Sallah Yayi Sabida Isasshen Lokaci Da Son Yin Ibadar, Amma Yanzu Sallar Muke Tarawa Tana Jiran Muyi ta Sabida Muna Ganin Ba Laifi Idan Mun Hade Su Alokaci Guda.
…………………………………
DAGA 1985 ZUWA YAU FA SUNE SHEKARA 40.
WANNAN SAUYIN ƘARARA YAKE KUMA MU MUKA CHANJA DUNIYA BA ITA TA CHANJAMU BA
……………………………….
SHEKARA 40 Masu Zuwa Ya kuke Tunanin
Abubuwa Yadda Zasu Kara Chanjawa ?
Wai Me Duniyar Nan Ke Rudar Mu Dashi Ne ?
Abinda Kafi Karfi Kiri Kiri Kana Kallo Yana Neman Fin Karfin ka Koma Yafi Karfin Ka, Wallahi Abu Biyu kadai Idan Muka Gyara Ya l Ishe mu Mu Ga Chanji.
1- MUJI TSORON ALLAH A CIKIN DUKKAN LAMURAN MU.
2- MU SADA ZUMUNCI DA TAIMAKON JUNA.
ALLAH YASA MUDACE.
Amen 🙏
Munasan muji raayinku gamada haka