GWANNAN KANO ABBA KABIR YUSUF YA KAFA KWAMITIN BINCIKEN KWAMISHINAN SUFURI NA JAHAR

GWANNAN KANO ABBA KABIR YUSUF YA KAFA KWAMITIN BINCIKEN KWAMISHINAN SUFURI NA JAHAR KAN BELIN WANI KASURGUMIN DILAN KWAYA

Belin dilan ƙwaya: Gwamna Yusuf ya umurci a binciki Kwamishinan sufuri na Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri na Jihar, Alhaji Ibrahim Namadi, game da rawar da ya taka wajen bayar da belin wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu.

Wannan umarni ya biyo bayan ce-ce-ku-ce da suka bulla daga al’umma bayan da rahotanni suka bayyana cewa sunan Kwamishinan ya bayyana a cikin takardun kotu da aka yi amfani da su wajen bayar da belin wanda ake zargin.

Sanarwar hakan ta fito ne a ranar Asabar daga mai magana da yawun Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Don magance lamarin, Gwamna Yusuf ya kafa kwamitin bincike na musamman da zai jagoranci binciken, wanda Shugaban kwamitin shi ne Barrista Aminu Hussain, mai ba Gwamna shawara kan harkokin Shari’a da Dokoki.

Kwamitin na da umarnin gano hakikanin abin da ya faru tare da bayar da shawarwarin matakin da ya dace a dauka cikin gaggawa.

‘Yan kwamitin sun haɗa da:

1. Barr. Aminu Hussain – Shugaba

2. Barr. Hamza Haladu – Mamba

3. Barr. Hamza Nuhu Dantani – Mamba

4. Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar – Mamba

5. Manjo Janar Sani Muhammad (Rtd.) – Mamba

6. Kwamared Kabiru Said Dakata – Mamba

7. Hajiya Bilkisu Maimota – Sakatariya

Yayin da yake bayyana kafa kwamitin, Gwamna Yusuf ya nuna damuwarsa matuƙa kan wannan zargi da ake yi, tare da sake jaddada aniyar gwamnatinsa na yaki da shaye-shaye da duk wasu miyagun dabi’u a fadin jihar Kano.

Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci bisa doka, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci cin hanci da rashawa ko take hakkin jama’a ba.

Daga wani bangare munji wasu lauyoyi da ra’ayin su nacewa balaifibane dan Kwamishina yakarbi beli akoto domin sharia akechigaba dayi dan haryanzu kotu bata gama shari’a ba dan haka mailaifi haryanzu yana kan zargine domin kotu bata gama shari’a ba

Allah yasa mudace me

Menene ra’ayinku

Munajira a comment section

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *