Ninafara sanar da duniya ankama dan wawu cewar jarimin kannywood Abdullahi Amdaz
Check kucedai ta barke a social media tun bayan sahannun karbar beli dan wawu da kwamishinan sufuri yayi Anata hayya hayya
A 2022 An Taba Kama Sulaiman Dan Wawu Da Katon 500 Na Tramadol,Saboda Nine Na Fara Sanar Da Kamen Nasa a Tiktok,Bayan Sp Kiyawa a Facebook,Har Mutane 41k Suka Kalla,Yaji Hau Shi,Pls Ku Karanta Cin Zarafin Da Yayi Mun
Dan Minning Abdullahi Amdaz Ban De San Alaqar Sa Da Wannan Shahararren Dilan Kwayar Ba,Amma Kafin Kwana 1 a Kama Ni Shine Ya Wallafa Hotona Yana Neman Wanda Ya Sanni,Kamar Yadda Zansa Muku Ku Gani.
Ranar 12/12/2022 Wani Mai Suna Abba Abdullahi Yazo Har Kwankwaso Yace Zai Tafi Dani,Nace Babu Inda Zani,Yace Waya Na Saya Ta Sata,Zamu Je Farm Center a Tabbatar,Shine Na Bishi Bayan Yayi Qaryar Daga CID Kano Yake
Maimakon Farm Center Nagannni a RRT Nayi Kwana 3,Duk Kwana 1 Saida Dan Wawu Yazo,Shida Da Matarsa,Da Abdullahi Amdaz,Wai Na Bata Musu Suna a Tiktok Aka Ganamun azaba Sosai Duk a Gaban Su,Akai Mun Wannan.
Daga Nan Aka Kaini Kotun PRP Qarqashin Alqali Nura Yusuf Ahmad Amma Alqali Bai Zauna Ba,Yace a Kawoni CID a Matsayin Court Oder(Ajiya)Nai Kwana 3,Muka Koma Kotun.
Ranar Talata Aka Karantamun Tuhumah,Wai Na Wallafa:”Nace Dan Wawu Yana Safarar Miyagun Kwayoyi,Tare Da Wallafawa a Tiktok Har Mutane 41,000 Sun Kalla”Har Suka Kawo Maganar Gidajen Radio Domin a Shedawa Duniya Sharri Nai Masa,Matarsa Tayi Hira,Inda Tace”Na Batawa Mijinta Suna,Tana Neman Kotu Tabi Mata Haqqinta,Na Kira Mijinta Dealer”
Alqalin Kotun Ya Aike Dani Zuwa Gidan Kurkuku Nayi Kwana 5,Aka Samu Akai Belina Bisa Conditions 6,Zan Iya Tuna,Dole Sai An Samu Ma’aikacin Gobnati Daga Grade 12 Zuwa Sama,Da Sa Hannun Mai Anguwa,Surety(Masu Karbata)Mutum 2,Sannan Kada Na Sake Hawa Social Media. kuma Kowanne Nau’in Media.
A tsakanin Haka,Abba Abdullahi(Police),Ya Kirani Tare Da Yayana a Wajen Kotu,Ya Kira Dan Wawu a Video Call a Lokacin Yana Qatar,Aka Tilastamun Akace Dole Saina Goge Manyan Accounts Dina Na Tiktok Mai Followers(87k Da Mai 19k),Naqi Yarda,Akai Mun Barazanar Zan Koma Pririzin,Sannan Aka Karbi Layuka na 3,2 Wadanda Na Bude Tiktok Account Din,Dayan Kuma Wanda Na Bude Email,Wai Don Kada Na Dawo Da Account Din,Kuma Akace Kada Nai Swapping Kamar Wani Me Mugun Lefi .
Muna Shari’a Da Dan Wawu,abunda Zai Baku Mamaki,Alqalin Fa Yasan An Kamashi Da Kayan,Amma Na Shafe Wajen Wata 4 Ina Zuwa Shari’a Ammar Shida Matarsa Basa Zuwa Dukda Criminal kes Ne,Amma Basa Turo Wakilci,Saide Kawai Alqali Ya Daga Karar Zuwa Wani Time Din.
Kwatsaam Wata Rana Ina Gida Abba Abdullahi Bazance Masa Karen Dan Sanda Ba,Amma Mai Yiwa Babban Mai Lefi Aiki,Yazo Ya Sake Kamani Har Daki Na,Da Sunan An Karya Beli Na,Naje Nai Kwana 2 matsayin Court Oder a CID,Sannan Na Wuche Prizin Nai Kwana 38,a Ciki Nai azumin 2023,Sannan Nai Zaben Gobna,a Ranar Azumi Yana 29 Na Fito.
A Taqaice Na Shafe Kusan Wata 11 Zuwa 13 Muna Shari’a Da Shahararren Dilan Kwaya Dan Wawu Akan Wai Sharri Nai Masa,Har Daga Qarshe Daya Kasa Kawo Shedar Abunda Yake Tuhumata Dashi,Sai Mai Gabatar Da Kara Aliyu Abideen Ya Buqaci A Bani Rantsuwa,Idan Ban Rantse Ba Kuma Kotu Tai Mini Tsatstsauran Hukunci,Tunda Na Qaryata Ni Ban Bata Masa Suna Ba,Bayan Karantamun Tuhumar.
Banda Alqalanmu Wasu Yan Sai a Hankali Ne Ina Aka Taba Yin Haka? Bayan M. Mai Tuhfah Yace:
“ولِلْيَمين أَيُّمَا إِعْمالِ … فيما يَكونُ مِنْ دَعاوِي المالِ”
Baiti Na(217) (باب اليمين وما يتعلق بها)
A Malikiyyah Alqali Ba Zai Bayar Da Rantsuwa Ba,Sai Cikin Abunda Yake Kudi Ne,Ko Abunda Yake Komawa Kan Kudin(Kadara),Ba Wai Akan Wanda An Kamashi Da Miyagun Kwayoyi Ba.
To Gashi Yanzu Bama Mutane 41k Ba Kusan Mutane Over 41m Sunsan An Kama Shi, Akan Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi,Kuma An Gurfanar Dashi a Gaban Federal High Court.
Sakayyah Daga Allah,Gashi Nan Kwana Kusan 50 a Prisin,Gashi Ma Ya Gudu Shida Matarsa
28/07/2025
Aljazirahausa.com.ng