MAZAUNA UNGUWAR ZANGO DA KOFAR MATA SUNA CHIKIN ZULIMI INDA RIGIMAR DABA YAKE TASIRI A UNGUWARNIN GADA BIYU ANATA CHIGABA DA FADACHE FADACHAN DABA ABUNDA YA JEFA MA ZAUNA CHIKIN DAMUWA
Fadan Daba Ya Tashi Tsakanin Zango da Kofar Mata a Birnin Kano
Wani kazamin rikicin fadan daba ya barke tsakanin matasa daga unguwannin Zango da Kofar Mata tun daren ranar Juma’a da misalin ƙarfe 3:00 na dare, lamarin da ya jefa mazauna yankunan cikin tsananin fargaba da tashin hankali.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an hango motoci da dama na jami’an ‘yan sanda a wurin, sai dai sun kasa ɗaukar wani mataki na dakile rikicin, inda suka koma kallo ba tare da tsoma baki ba.
Wani matashi da aka tattauna da shi, Abubakar Abdullahi, ya ce wannan rikici na yawan faruwa kuma gwamnati ce kaɗai za ta iya kawo ƙarshensa idan har an daure damara.
“Ya kamata gwamnati ta shiga tsakani don kawo karshen wannan rikici da ya zama tamkar jiki ya ƙafe,” in ji shi.
Mazauna unguwar dorayi sunata chigaba da harkokinsu musamman kananan yan kasuwa wanda abaya fadan daba daya hanasu gudanar da kasuwancinsu sabida zaman dardar da ake sabida masu kwachan waya da fadan daba yanzu lamarin ansamu sauki a unguwar dorayi duba da irin namijin kokari da Jami’an tsoro suke a unguwar dama babban titin unguwar inda akechigaba da sintiri
Allah ya kawo zaman lafiya maidorewa
Jaridar aljazirahausa na ci gaba da bibiyar halin da ake ciki domin kawo muku sabbin bayanai kai tsaye daga yankunan da abin ya shafa.