Manchester United ta chigaba da zawarchin Benjamin sesko

‍MANCHESTER UNITED TA BAZA KAIMI WAJAN TAGA TASAMU DAMAR DAUKAR GWARZAN DAN WASANNAN BENJAMIN SESKO A INDA NEWCASTLE TASHIGO DA KARFINTA KAN ZAWARCHIN DAN WASAN A YAUDAI AKE SA RAN AGENT DINSA ZASU TATTAUNA KAN WACHE UNGIYA YAKE DA RAAYIN KOMAWA

BENJAMIN ŠEŠKO TRANSFER SAGA

SHAHARARREN DAN JARIDA DAN KASAR GERMANY Fabrizio Romano ya fitar da sabuwar sanarwa game da fafatawar neman Benjamin Šeško.

 

Newcastle sun gabatar da tayin sayen shi, amma RB Leipzig sun ƙi amincewa. Sai dai Newcastle sun nuna shirinsu na biyan duk wani farashi idan har Šeško ya yarda ya zaɓe su.

A bangare guda kuwa, Manchester United sun sake bayyana wa RB Leipzig zasu tura tayinsu a hukumance cewa zasu nan take, muddin Šeško ya bude ƙofar shigowa Old Trafford.

Yanzu haka, wakilin Šeško yana Leipzig tare da dan wasan don su gudanar da muhimmiyar tattaunawa kai tsaye da nufin tura gaba kai ƙarshe akan shawarwari.

Duk da rahotannin da ke fitowa daga Slovenia da ke cewa wai tuni Šeško ya zabi Newcastle, Romano ya jaddada cewa lamarin har yanzu yana a kashi 50/50 ne tsakanin United da Newcastle.

“Da zarar Šeško ya bayyana cewa ‘Ina son zuwa wannan kulob din,’ to labarin zai ɗauki sabuwar hanya mai sauki. Amma kafinn nan, tayin da ake turawa bazai sauya komai ba.”

A cikin awanni 24 zuwa 48 masu zuwa, ana sa ran Benjamin Šeško zai yanke hukunci na ƙarshe.

AKAN KOMA WARSA NEWCASTLE KO MANCHESTER UNITED


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *