Gwamnan jihar Kano yabawa hukumomin tsore dama subunchiko wanda suka kashe Sadiq gentle

GWAMNAN JIHAR KANO ALH ABBA KABIR YUSUF YA UMURCI HUKUMOMIN TSARO SU GAGGAUTA KAMA WAƊANDA SU KAI SANADIYYAR MUTUWAR SADIQ GENTLE

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarni ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da bincike tare da kama wadanda suka aikata kisan gilla ga hadiminsa na musamman kan harkokin kafafen sada zumunta, Marigayi Sadiq Gentle.

Marigayi Sadiq Gentle ya rasu ne sakamakon raunukan da ya samu bayan wani mummunan hari da wasu ‘yan ta’adda suka kai masa a gidansa, inda suka sare shi da adda. Ya ce ga garinku da safiyar yau, Alhamis, a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana rasuwar Sadiq Gentle a matsayin babban rashi ga gwamnatin Kano da ma al’ummar jihar baki ɗaya.

“Labarin rasuwar Sadiq Gentle ya girgiza ni matuƙa, ya kuma cika ni da baƙin ciki da ƙunci. Ya kasance ƙwararre, mai kishin ƙasa, mai himma da jajircewa wajen aikinsa, musamman a fagen sadarwa da kafafen zamani,” in ji Gwamnan.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai bayyana shi da cewa: “Mugun aiki ne, na dabbanci, kuma abin ƙyama ne da ba za a taɓa lamunta da shi ba.”

Ya kuma mika saƙon ta’aziyya na musamman ga iyalan marigayin, abokansa da abokan aikinsa, yana mai tabbatar musu da cewa Gwamnatin Jihar Kano na tare da su a cikin wannan mawuyacin hali da suka tsinci kansu.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an tabbatar da adalci ga marigayi Sadiq Gentle, tare da hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Abaya bayannan sha,anin fadan daba da masu kwachan waya yayi tsamari a Jahar Kano  shin  wannan umarni da Gwamnan yabayar ko zaasamu sauki Allah yasa mudace

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *