KAMFANIN JIRGIN SAMA YADAKATAR TA DAUKAR WATA FASINJA BIYO BAYAN MARI DATA YIWA MA AIKACHIR

  1. KAMFANIN JIRGIN SAMA IBOM AIR YADAKATAR DA DAUKAR WATA FASINJA BIYO BAYAN MARIN  MA AIKACHIRYARSA DA TAYI

Kamfanin jirgin Ibom Air ya dakatar da fasinja daga hawa jiragen sa

Kamfanin jirgin sama na Ibom Air, ya dakatar da Comfort Emmanson daga hawa jiragen sa saboda cin zarafin ma’aikaciyar jirgin, wanda ya ke jigilar Uyo zuwa Lagos a filin jirgin saman Lagos a jiya Lahadi.

Kamfanin jirgin, cikin wata sanarwa a yau Litinin, ya ce ba za a sake baiwa wannan fasinja damar hawa kowane jirgin sa ba daga yanzu.

“An fitar da fasinjar daga jirgin sannan aka mika ta ga jami’an tsaron FAAN, kuma daga nan aka mika ta ga Rundunar Ƴansanda don ci gaba da bincike,” in ji Ibom Air.

Bidiyoyi da suka yadu sun nuna Emmanson tana dukan ɗaya daga cikin ma’aikatan jirgin yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin rike ta.

Ibom Air ya ce, “Ta ƙi bin ƙa’idojin shiga jirgi, sai bayan da matuƙin jirgi ya yi sanarwa da a kashe waya, sai ta ƙi kashewa, shine wani fasinja da ke zaune a gefenta ya ɗauki wayar ya kashe ta.

“Wannan abin ne ya batawa Emmanson rai har ta fara zagi. Daga baya an shawo kan lamarin, jirgin ya tashi kamar yadda aka tsara.

“Da suka isa Lagos, sai Emmanson ta jira duk sauran fasinjoji su sauka ‘, daga bisani sai ta bi wata ma’aikaciyar jirgin wacce ta ce ta lashe wayar ta tun da fari.

” Ta matsa kusa da ita ba tare da ta ankara ba, ta taka mata ƙafa, ta tsinke mata gashin kan ta, ta cire mata tabarau ta jefar a ƙasa, sannan ta rika dukan ta da takalmi.

Channels TV ta rawaito cewa kamfanin na Ibom Air ya riga ta miƙa rahoton lamarin ga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA).”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *