HUKUMA ALHAZAI TAKASA TA SANYA ADADIN KUDIN AIKIN HAJJI NA SHEKARA MAIZUWA

HUKUMA ALHAZAI TAKASA TA SANYA ADADIN KUDIN AIKIN HAJJI NA SHEKARA MAIZUWA 2026

Hukumar jin dadin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da kudin da alhazai za su fara biyan da kuma adadin kujerun da aka baiwa Kano na Hajjin 2026

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta bayyana kudin ajiya ga maniyyatan jihar da za su yi aikin Hajjin shekarar 2026.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Sulaiman A. Dederi, ya fitar ta ce, wannan mataki ya yi daidai da umarnin Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON).

Ya bayyana cewa Babban Daraktan hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin taron da aka gudanar tare da mambobin hukumar, manyan jami’ai, jami’an cibiyoyin hajjin kananan hukumomi da sauran ma’aikata a ofishinsa.

Dederi ya ce, bisa ga umarnin NAHCON, an sanya kudin ajiya na aikin Hajjin 2026 kan naira miliyan 8,500,000.

Ya kara da cewa hukumar za ta fara karɓar kudaden ajiya ta hanyar banki, ta wajen jami’an cibiyoyin hajjin kananan hukumomi.

Haka kuma ya bayyana cewa jihar Kano ta samu kujeru 5,684 domin aikin Hajjin 2026.

Ya ce za a fara karɓar kudin ajiya nan da nan, kuma za a ci gaba da karɓa har zuwa ranar 5 ga Oktoba, 2025, lokacin da za a sanar da kuɗin aikin Hajji na ƙarshe.

“Alhaji Lamin Rabi’u ya ja hankalin dukkan maniyyatan da su gaggauta biyan kudin ajiyarsu bisa jadawalin da masarautar Saudiyya ta bayar domin aikin Hajjin 2026. Ya kuma nanata cewa dole ne dukkan maniyyata su gabatar da hotuna guda takwas masu girman fasfo da ingantaccen fasfo na ƙasa da ƙasa a matsayin wani ɓangare na tsarin rajista.

“A nasa jawabin, Shugaban kwamitin gudanarwar hukumar, Alhaji Yusif Lawan, ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da Ya ba wa dukkan maniyyata ikon biyan kudin aikin Hajji ba tare da wahala ba.

Amen  aljazirahausa.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *