Dan wasan Manchester United na tsakiya kobbie Mainoo zaibar kungiyar karshan shekarar nan

Labarin-wasanni

Na wannan mako inda zakuji kungiyoyi dadama suna zawarchin kobbie mainoo

Ƙungiyoyin Saudiyya na son Bruno Fernandes, Erik ten Hag zai koma Ajax, Napoli ce kan gaba a zawarcin Mainoo, Barcelona da Liverpool na son Upamecano, Arsenal Zata sayar da Jesus, Newcastle na son dawo da Anderson, Palace, Madrid, Barcelona, Chelsea da United na hamaayya kan Kees, Palace na son rike Kamada, Munich na son Timber, Neuer na son ci gaba da taka leda, City na son daukar Molina

 

Manchester United ta kuduri aniyar ci gaba da rike kyaftin din ta Bruno Fernandes mai shekaru 31 a kasuwar musayar ‘yan wasa ta watan Janairu, duk da cewa kungiyoyin Saudiyya na son yin zawarcin dan wasan tsakiyar na Portugal. (Manchester Evening News)

 

Napoli ce kan gaba wajen sayen dan wasan tsakiya na Manchester United da Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, a watan Janairu. (Tuttomercatoweb)

 

Barcelona na shirin yin hamayya da Liverpool don siyan dan wasan bayan Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 26, lokacin da kwantiraginsa zai kare a Bayern Munich a bazara mai zuwa. (Fichajes)

 

Arsenal za ta amince da tayin kusan fan miliyan 30 kan Gabriel Jesus, mai shekara 28, wanda Everton ke zawarci. (Teamtalk)

 

Newcastle za ta so a dawo da dan wasan tsakiyar Nottingham Forest da Ingila Elliot Anderson, mai shekara 22 zuwa kulob din bayan ta sayar da shi watanni 16 da suka wuce. (Mail)

 

Manchester City na sa ido kan yanayin dan wasan bayan Atletico Madrid da Argentina Nahuel Molina, mai shekara 27 ke ciki. (Teamtalk)

 

Crystal Palace na nuna sha’awar siyan dan wasan tsakiya na AZ Alkmaar Kees Smit, mai shekaru 19, wanda ya bugawa Netherlands wasa a matakin ‘yan kasa da shekaru 19 kuma ya ja hankalin ‘yan kallo daga Real Madrid, Barcelona, Chelsea da Manchester United. (Mail)

 

Tsohon kociyan Manchester United Erik ten Hag na iya komawa bakin aiki don maye gurbin Johnny Heitinga a tsohon kulob dinsa na Ajax bayan barin Bayer Leverkusen. (De Telegraaf)

 

Crystal Palace na son dan wasan tsakiya na Japan Daichi Kamada, mai shekara 29, ya tsawaita zamansa a Selhurst Park da kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa. (Sky Sports)

 

Bayern Munich na daya daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan baya na Arsenal dan kasar Holland Jurrien Timber, mai shekara 24, wanda ya bude tattaunawa kan sabunta kwantaraginsa. (Caughtoffside)

 

Golan Bayern Munich dan kasar Jamus Manuel Neuer, mai shekara 39, yana tunanin tsawaita shekarunsa na murza leda fiye da 2026, inda ake tunanin zai tsawaita zamansa. (Bild)

 

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi, ko ya dace United ta ci gaba da zaman da Fernandes?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *