Anyi yunkurin yin juyin mulki a Najeriya makwannin baya da suka huce tun bayan zargin yin hakan tunidai shugaban kasa Bola Ahmed tinubu ya dauki matakin sauke hafsoshin kasarnan inda aka maye gurbinsu da wasu sababbin
Sojoji sun fara binciken zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu inda suka yiwa gidan tsohon Gwamnan Bayelsa ƙawanya
Masu bincike na rundunar soji sun tsare wani Daraktan Gudanarwa na hukumar gwamnatin tarayya da ke Kudu maso Kudu bisa zargin hannu a cikin shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Rahotanni sun ce an kama shi ne bayan ya aika da kuɗi masu yawa zuwa ga tsohon karamin Ministan Harkokin Mai, Timipre Sylva, wanda ake zargin yana daga cikin masu tallafawa juyin mulkin.
Majiyoyi sun bayyana cewa an kai samame gidan Sylva da ke Abuja a ranar Asabar, inda aka kama ƙaninsa, Paga, da direbansa, yayin da shi Sylva ke ƙasashen waje.
An ce ya fasa dawowa Najeriya bayan samun labarin kama shugabannin juyin mulkin.
Sai dai jami’an hulɗa da jama’a na rundunar soji, Manjo-Janar Markus Kangye da Birgediya-Janar Tukur Gusau, ba su amsa kiran wayar ‘yan jarida ba kan batun.
A baya, rundunar soji ta tabbatar da tsare jami’ai 16 saboda karya dokokin aiki da rashin ladabi, amma rahoton SaharaReporters ya nuna cewa jami’an daga matakin Kyaftin zuwa Birgediya-Janar ne ake zargin suna shirin kifar da gwamnati. inda yanzu tuni ankafa kwamitin binchiken akan musabbabin hakan
Allah ya bamu zaman lafiya maidorewa amen