1 RUNDUNAR SOJI AMURKA TAMIKA BAYANAI KAN MATAKIN DA YAKAMATA TA DAUKA AKAN NAJERIYA
Kamar yadda jaridar New York Times ta ruwaito, rundinar Sojin Amurka mai lura da bangaren Afirka US Africa Command (AFRICOM) ta mika matakai guda uku zuwa ga cibiyar kula da harkokin yaki na Amurka (Department of War) wanda ya kamata Donald Trump ya dauka a kan Nigeria
Shugaban Amurka Donald Trump ne ya bada umarni wa rundinar Sojin Kasar suyi nazarin irin matakan da ya kamata a dauka akan Nigeria saboda wai ana yiwa Kiristoci ki$an kare dangi
Matakai guda uku da rundinar ta ce a dauka sun hada da:
(1) Mataki mai tsanani: Girke manyan jiragen yaki wanda zasu dinga jefa manyan bama-bamai masu cin nisan zango a sansanonin ‘yan ta’adda dake Arewacin Nigeria, wannan matakin yana bukatar kafa sansanin Sojin Amurka a cikin Nigeria
(2) Mataki mai tsaka-tsaki: A dauki matakin amfani da jiragen yaki marassa matuki wanda suka hada da MQ-9 Reaper da MQ-1 Predator domin a dinga bugun sansanin ‘yan ta’adda, tawagarsu da kuma ababen hawansu, shima wannan yana bukatar kafa sansanin Soji amma ba dole sai a cikin Nigeria ba
(3) Mataki mai sauki: Za’a hada rundinar tsaro na hadin gwiwa tsakanin dakarun Amurka da Nigeria wanda ya shafi musayar bayanan sirrin tsaro, horo da tallafin kayan aiki da sufuri domin kaddamar da hari akan B0k0 Har@m da barayin daji masu garkuwa da mutane, wannan matakin yana bukatar kafa sansanin Sojin Amurka a cikin Nigeria
Sai dai wasu jami’an cibiyar tsaro na Amurka sun ce wadannan matakai ba zasu kawar da matsalar tsaron Nigeria wanda zai sa a dena kashe Kiristoci ba, dole sai Amurka ta dauki matakin yaki a cikin Nigeria irin wanda tayi a Kasashen Afghanistan da Iraqi
Wannan shine halin da ake ciki a cewar jaridar New York Times, ana jiran matakin da Donald Trump zai dauka kafin a fara
Azahiri dai matakan inda da gaske manufarsu kenan kawar da ta’addanci to suna da kyau, kuma duk mai kaunar zaman lafiyar Nigeria zai aminta da su, to amma tarihi ya tabbatar da cewa Amurka bata taba shiga wata Kasa yaki da sunan kawar da ta’addanci aka samu zaman lafiya ba, sai ma kara |a|ata lamura da kuma satar dukiyar Kasa
Sannan abinda ya kamata mu tambaya shine, a bangaren kudancin Nigeria ana fama da matsalar ‘yan tawaye masu fafutukar kafa kasar Biyafara, suna ta ka$he ‘yan uwansu Kiristoci,.amma rundinar Sojin Amurka bata mika bayanan daukar mataki a kansu ba, sai yankin Arewacin Nigeria, don haka idan akace tana da wata boyayyar ajanda ne akan Arewa ba za’a musa ba
Yaa Allah karka basu damar hulakanta Najeriya yaa Allah wani dayake da hada baki akan A yaki Najeriya Allah kawu lakantasu karka basu dama akan karsarmu Najeriya
Allah katsare kasar mu dan isar annbi Allah katarwatsa mulkin kafurchi da kafurai Amen