TURKA TURKA TA BALLE TSAKANI DEPUTY SEN PRESIDENT BARAU JIBRIN MALIYA DA TSOHON CHIYAMAN NA KARAMAR HUKUMAR UNGOGGO ABDULLAHI GARBA RAMAT

TUN BAYAN CHIKAS DA AKASAMU NA TABBATAR DA ENG ABDULLAHI GARBA RAMAT DA MAJALISAR DATTAWA TAYI

ABUN YAZAMA SIYASA

Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya nesanta kansa daga masu yada jita-jita kan Matsala tsakanin sa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

Injiniya Abdullahi Garba Ramat, wanda Shugaban Ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da sunan sa a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC), ya fito fili ya nesanta kansa daga jita-jitar da ake yadawa cewa yana da matsala da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da kuma Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Injiniya Ramat ya ce yana girmamawa da mutunta manyan shugabannin majalisar tare da sauran ‘yan majalisar gaba ɗaya. Ya bayyana cewa labaran da ake yadawa cewa yana akwai takun saka tsakaninshi da shugabannin majalisar “ba su da tushe, kuma ƙarya ce tsagwaron ta.”

“Tun daga lokacin da aka sanar da nadin da aka yi min, Sanata Barau Jibrin shi ne mutum na farko da ya kira ni don taya ni murna, kuma tun daga wancan lokaci yana nuna mini ƙauna da goyon baya. Shi ma Sanata Akpabio ya karɓe ni da hannu biyu a lokacin da muka haɗu tare da Sanata Barau, inda ya yaba da yadda gwamnati ke bai wa matasa dama a tsarin gwamnati,” in ji Ramat.

Ya ƙara da cewa, lokacin da aka jinkirta tabbatar da nadinsa na ɗan lokaci, Sanata Barau ne ya kai shi ofishin Shugaban Majalisar Dattawa domin ya bayyana masa halin da ake ciki. “A wannan lokacin Sanata Akpabio ya karɓe ni cikin fara’a, ya kuma tabbatar mini cewa rahoton tabbatardani zai zo cikin lokaci. Gaskiya, dukkan su sun nuna min adalci da mutunci,” in ji shi.

Injiniya Ramat ya kuma yaba da yadda Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Wuta, ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin, ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya da mutunci ba tare da wani nau’in matsin lamba ko neman wani abu daga gare shi ba. “Har ma shugaban kwamitin ya taimaka min wajen fitar min da wasu takardu na, abin da ya nuna irin sauƙin kai da kishin kasa da suke da shi,” inji Ramat

Ya kuma ambaci yadda wasu sanatoci irin su Enyinnaya Abaribe, Kawu Sumaila, Rufa’i Hanga, da Bashir Garba Lado suka nuna masa goyon baya da shawarwari masu amfani, yana mai cewa “abin da ya gani a Majalisar Dattawa ya ƙara masa imani da ɗaukakar majalisar da haɗin kan ƙasa.”

Sai dai Injiniya Ramat ya nuna bacin ransa kan yadda wasu mutane ke ci gaba da amfani da sunansa wajen shirya taruka, bayyana ra’ayoyi, da fitar da bayanai na siyasa ba tare da izinin sa ba.

“Na riga na wallafa sanarwar ƙaryata wannan jita-jita tun ranar farko, na kuma roƙi mutane da su kwantar da hankali. Amma abin takaici, maimakon a daina, sai wasu suka ci gaba da ƙara haifar da rudani. Ina so in bayyana wa duniya cewa ban ba kowa izinin yin jawabi, taro, ko sanarwa a madadina ba,” in ji shi.

Ya gargadi masu ci gaba da amfani da sunansa cewa zai ɗauki matakin doka idan abin ya ci gaba, yana mai jaddada cewa babu wata takaddama tsakaninsa da wani daga cikin shugabannin majalisar.

Injiniya Ramat ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewar da ya nuna masa, tare da jinjinawa majalisar dattawa saboda yadda ta gudanar da dukkan matakai cikin gaskiya da adalci.

“Ina nan da cikakken goyon baya na ga manufar Renewed Hope Agenda da Shugaban Ƙasa ke jagoranta, ina kuma da girmamawa ga jagorancin Majalisar Dattawa da kuma himma ga haɗin kan ƙasa da kyakkyawan mulki,” in ji shi.

Sanarwar ta kawo ƙarshen jita-jitar da ta mamaye kafafen sada zumunta kwanakin baya, inda wasu ke yada labarai cewa Injiniya Ramat na cikin sahun masu sukar jagorancin majalisar dattawa.

MU SAIDAI MUCE  ALLAH YA FUDDA NADAURE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *