HUKUMAR ILIMIN BAI DAYA TA JIHAR KANO (SUBEB). TANA SANAR DA AL’UMMAR KADA A YAU DARESU WAJAN KARBAR KUDI DA ZUMMAR ZAA SAMOMUSU AIKI

SANARWA TA MUSAMMAN DAGA HUKUMAR ILIMIN BAI DAYA TA JIHAR KANO (SUBEB).

 

Biyo bayan samun wasu rahotanni cewa wasu mutane na ƙoƙarin damfarar masu neman aikin koyarwa ta hanyar buƙatar su ba da wasu kuɗaɗe da sunan za su taimaka musu su samu nasarar jarabawa, Hukumarmu ta ɗauki wannan batu da matuƙar muhimmanci.

 

Haka kuma, mun samu bayanai cewa wasu na yin shisshigi wajen fitar da sanarwar bogi da ba su fito daga Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Kano ba.

 

Saboda haka, muna sanar da al’umma cewa Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ba ta da wata alaƙa ko hannu a duk wani yunƙuri na neman kuɗi domin samun nasara a jarabawar daukar malamai.

 

Hukumarmu tana gargadin duk masu wannan mummunan yunƙuri da su daina, domin an fara bincike kan lamarin, kuma za a ɗauki matakin shari’a kamar yadda doka ta tanada.

 

Muna kuma ƙara jaddada cewa duk mai bayar da kuɗi da mai karɓa laifi suke aikatawa, kuma Hukumar za ta hukunta duk wanda aka samu da laifi.

 

Har ila yau, muna sanar da jama’a cewa Hukumar Ilimin Bai Ɗaya tana da ingantaccen tsarin sanarwa, don haka muna kira ga al’umma da su guji amfani da kowace sanarwa da ba ta fito daga Hukumar ba.

 

Hukumarmu tana kuma sanar da cewa za a gudanar da jarabawar kamar yadda aka tsara, wato a ranar Asabar 10 da Lahadi 11 ga wata.

 

Bugu da Kari, Hukumarmu na sanar da cewa sai waɗanda sunayensu suka fito tare da lambar jarabawa (Examination Number), Username da Password kaɗai za su halarci jarabawar.

Sanarwa daga:

Balarabe Danlami Jazuli Daraktan Sashen Lura da Harkokin Sadarwa na SUBEB, a madadin Shugaban Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Kano Malam Yusuf Kabir.

To jama,a sai akiyaye sabida gudun yan, wankiya Allah yasa mudace

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *