GWAMNATIN JIHAR KANO ZATA GWAN GWAJE MALAMAI DA RANCHAN KUDI DAN SU MORE RAYUWAR

Gwamnatin jihar Kano zata gwan gwaje malaman primary da na secondary da ranchan kudi dan suse ababan hawa dan more rayuwa

Gwamnan Jihar Kano, Alh Abba Kabir Yusuf, ya sanar da bayar da rancen Naira miliyan 200 ga malaman makarantun sakandare da na firamare a fadin jihar. Wannan rance na da nufin bai wa malamai damar siyan ababen hawa domin saukaka musu zirga-zirga zuwa wuraren aikinsu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron da ya gudana, inda ya ce wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnatin sa na inganta jin dadin malamai da kuma karfafa tsarin ilimi a jihar. Ya kuma bukaci malamai da su yi amfani da damar da kyau, tare da bayar da gudunmawa wajen inganta ilimi a Kano.

Wannan mataki na nuna goyon bayan gwamnati ga malamai zai taimaka wajen kara kwarin gwiwa da inganta aiki a fannin ilimi, wanda hakan zai amfanar da dalibai da al’umma baki daya.
Duba da yanayi da ake chiki gwamnan ya tausayawa musu dan suchigaba da rayuwa maikyau da inganchi a jahar

Aljazirahausa.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *