JAM’IYYAR APC  NAKARA SAMUN FARIN JINI AD IDON YAN JAM.IYAR

DA ALAMU KUJERAR SHUGABAN JAM’IYYAR APC  NAKARA SAMUN FARIN JINI AD IDON YAN JAM.IYAR

Ana ci gaba da matsin lamba wa Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, akan ya yi murabus daga kujerarsa domin karɓar kujerar Shugaban jam’iyyar APC mai mulki, bayan murabus ɗin Dr. Abdullahi Umar Ganduje’

Jaridar THISDAY ta gano cewa, bayan Ganduje ya ajiye mukaminsa a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, ƙarfafa kira na fara bayyana daga jiga-jigan jam’iyyar daga yankin Arewa ta Tsakiya (North-Central), suna rokon a mayar da kujerar Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa ga yankinsu, bisa tsarin rabon mukamai da aka kafa a 2022,

Sai dai mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin watsa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, a daren Asabar ya bayyana cewa babu wani canji da aka yi ga matsayin Akume a matsayin SGF.

“Bayanan da ke yawo cewa an sauya Akume ba gaskiya ba ne. Wadanda ke yada labaran ƙarya ne suka kirkira hakan. Fadar shugaban ƙasa na shawartar ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan labarin ƙarya,” in ji Onanuga.

Rahotanni sun nuna cewa matsin lambar da ake yi wa Akume na da nasaba da sabon kiraye-kirayen jiga-jigan APC daga Arewa ta Tsakiya, da ke son a dawo da kujerar shugaban jam’iyya ga yankin, bayan Ganduje daga Arewa maso Yamma ya yi murabus.

A baya, yankin Arewa ta Tsakiya (inda Akume ya fito) ta rasa kujerar bayan murabus ɗin Sanata Abdullahi Adamu, wanda hakan ya ba Ganduje damar hawa kujerar a watan Agusta, 2023, yayin taron kwamitin NEC na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.

Bayan Ganduje ya yi murabus bayan watanni 22 yana jagorantar APC, Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa shiyyar (Arewa), Hon. Ali Bukar Dalori, ya ɗauki rikon kwarya na kujerar shugaban jam’iyyar, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada. Dalori zai rike mukamin har zuwa watan Disamba, lokacin da kwamitin NEC zai nada sabon shugaban jam’iyyar na dindindin.

Kodayake wasu kungiyoyi daga Arewa ta Tsakiya sun nuna adawa da nadin Ganduje a baya, a taron NEC na watan Fabrairu an tabbatar da nadin nasa tare da cigaba da bai wa yankin Arewa maso Yamma wannan kujerar.

Yanzu da Ganduje ya yi murabus, wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar daga Arewa ta Tsakiya sun sake komawa ga yunkurin ganin an dawo da kujerar shugabancin jam’iyya gare su.

Ko da yake Akume bai bayyana sha’awar neman kujerar shugaban APC ba, THISDAY ta rawaito cewa akalla sunayen mutane biyar daga yankin Arewa ta Tsakiya na yawo a matsayin masu zawarcin wannan kujera.

Sun hada da:Tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umar Tanko Al-Makura

Tsohon gwamnan Jihar Filato, Sanata Joshua Dariye

Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello

Sanata Solomon Ewuga

Sanata Sani Musa, wanda ke wakiltar yankin Sanatan Gabashin Neja a majalisar dattawa.

Dama wasu. Nada sha.awar tsayawa neman takarar shugaban jam’iyyar APC

Awata Disamba ne 2025 ake saran zaa shiga zaben kujerar shugaban jam’iyya APC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *