KAMFANIN MOTA NA TESLA YA KARA SABUWAR FASAHA INDA YAYI MOTAR DA INDAN KASIYETA ITACHE ZATA KAWO KANTA GURIN WANDA YASIYETA

KAMFANIN MOTA NA TESLA YA KARA SABUWAR FASAHA INDA YAYI MOTAR DA INDAN KASIYETA ITACHE ZATA KAWO KANTA GURIN WANDA YASIYETA HAR GIDA

Motar kamfanin Tesla ta tuƙa kan ta zuwa gidan wanda ya saye ta

Kamfanin ƙera motoci na Tesla ya tura motar da ya ƙera zuwa gidan wanda ya saye ta ita kaɗai ba tare da direba ba, a karon farko.

A wani bidiyo da kamfanin ya saki, an ga motar samfurin Model Y ta tashi daga kamfanin a birnin Austin na jihar Texas a Amurka zuwa gidan wanda ya saye ta, tafiyar rabin sa’a ba tare da direba ko fasinja a cikinta ba.

Kamfanin Tesla bai yi wani bayani kan fasahar da ya yi amfani da ita a wajen ƙera motar ba.

Sai dai a cikin bayanan yadda ake sarrafa motocin Tesla, samfurin Y, akwai tsarin yadda motar za ta iya tuƙa kanta da kanta (tare da sa idon wani), kuma za a iya bai wa motar umarnin tuƙa kanta ne kawai a lokacin da direba ke cikinta, ta yadda zai iya ci gaba da tuƙawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Sai dai a bidiyon da kamfanin ya saki na yadda motar ta kai kanta gidan mai ita, ya nuna cewa babu kowa a cikinta.

Shugaban kamfanin na Tesla Elon Musk ya ce babu wani da ya sanya hannu daga waje, wajen ganin motar ta isa gidan wanda ya saye ta.

A ƙarshen bidiyon an ga motar ta tsaya a kofar gida, inda mai ita da wasu ma’aikatan kamfanin ke tsaye suna jiran ta.

Sai dai masu kallon ƙwaƙwaf a shafukan sada zumunta sun ce sun gano cewa motar ta tsaya a wurin da ba a amince mota ta yi fakin ba.

Bayan isar motar, Elon Musk ya gode wa ma’aikatan kamfanin bisa aikin da suka gudanar, inda ya rubuta a shafin X cewa: “A iyakar sani na, wannan ne karon farko da mota ta tuƙa kanta da kanta a kan babban titi ba tare da sanya hannun ɗan’adam a ciki ko a waje ba.”

Sai dai akwai kuskure a wannan kalami nasa, kasancewar motocin Waymo – wanda wani ɓangare ne na kamfanin Alphabet (mallakin Google) – kan yi safarar ma’aikatan kamfanin a biranen Phoenix da San Francisco da kuma Los Angeles na Amurka ba tare da direba ba kuma sukan bi manyan tituna.

SHIN MU YAN NAJERIYA ZAMU IYA AMFANI DA MOTAR NAN AKAN TITINAN MU MUHADU A COMEN SECTION

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *