GWAMNATIN JIHAR KANO TANA GUDANAR DA TARO KAN CHANJA KUNDIN TSARIN MULKIN JAHAR
TARON TATTAUNAWA DA MASU RUWA DA TSAKI KAN GYARAN KUNDIN TSARIN MULKIN ƘASA
Gwamnatin Jihar Kano ta shirya taron masu ruwa da tsaki (Stakeholders Engagement Meeting) domin tattaunawa kan gyaran kundin tsarin mulki, tare da samar da matsayar jihar kafin gudanar da taron jin ra’ayin jama’a da Majalisar Dattawa za ta shirya nan gaba.
Taron ya haɗa manyan wakilai daga sassa daban-daban na al’umma, ciki har da:
• ’Yan majalisar jiha da na ƙasa
• Kungiyoyin fararen hula da lauyoyi
• Shugabannin addini da na gargajiya
• Kungiyoyin ƙwadago da ƙwararru (NLC, TUC, NBA, NUT, NUJ, NMA, da sauransu)
• Masu ruwa da tsaki daga harkokin kasuwanci da kafafen yaɗa labarai
• Tsofaffin da sabbin masu rike da mukaman siyasa
Manufar taron ita ce tattauna muhimman sassa na kundin tsarin mulkin da ke bukatar sauyi, da kuma samar da cikakkiyar matsayar jihar Kano da za a gabatar a taron jin ra’ayin jama’a na Majalisar Dattawa.
Wannan mataki na nuna aniyar Gwamnatin Kano wajen tabbatar da tsarin mulki da ke da tasiri ga rayuwar al’umma, da kuma bai wa jama’a damar yin tasiri a cikin tafiyar da mulki.
Inda taran hada da manya masu ruke da mukamai
Tsowan gwamna eng rabiu musa Kwankwaso
Tare da yan majalisar tarayya da najaha Da sarkin Kano malam Muhammad sunusi ii da sarkin rano da sarkin gaya da sarkin karaye
Dan yan majalisar jahar da kwamishinoni da mataimakin gwamna da sectary Gwamnatin da shugaban fadar gwamnatin kano dr suleiman sani da shuran manyan yan siyasa