Kwamishinan gwamnatin jihar Kano Ibrahim namadi dala yayi belin babban dilan kwaya

DA DUMI DUMI:

Kwamishinan gwamnatin jihar Kano Ibrahim namadi dala yayi belin babban dilan kwaya

kwamishina Namadi Yayi Belin Shararren Dilan Miyagun Kwayoyi Sulaiman Dan Wawu Fagge. Wanda yashara wajan shigo da miyagun kwayoyi

Cikin Gaggawa Ya Kamata Alhaji Abba Kabir Yusuf Yayi Gaggawar Dakatar Da Hon Ibrahim Namadi,Saboda Abunda Yayi Ba Qaramin Kuskure Bane,Kuma Hakan Zai Iya Shafar Farin Jinin Kwankwasiyyah a Nigeria,a Maimakon Aga Qoqarin Abba Kabir Yusuf Wurin Yaqi Da Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi,Za’aga Ai Daurewa Harqallar Kwayoyin Gindi Yake Ta Bayan Fage.

Mai Shari’ah M.S Shu’aibu Na Federal High Court(Court Number 1),Ya Yarda Zai Bayar Da Belin Sulaiman Dan Wawu Tun Ranar 16/07/2025,Amma Yayi Tsauri Matuqa,Wanda Hakan Ke Nuna Shi Kansa Ba Belin Yakeson Ya Bayar Ba,Wanda Cikin Condition Na Belin,Dole Wanda Zai Karbe Shi Ya Zama Yana Da Muqamin Commissioner a Jaha,Ko Kuma Member Cikin Kwamitin Zartarwa,Sanann Idan Ya Samu Daya Cikin Wadannan ,Zai Ajjiye Miliyan 5,Shi Kuma Wanda Ake Zargi Zai Yi Belin Kansa a Miliyan 3.

Abun Mamaki,Abun Baqin Ciki,Abun Allah Wadai,Abun Takaici Ranar 18/07/2025 Kwamishinan Mai Girman Gobnan Kano,Hon Namadi Salon Ya Shafawa Gobnatin Abba Baqin Jini,Ya Rubutawa Babbar Kotun Tarayyah Dake Nan Kano,Zai Tsayawa Sulaiman Dan Wawun.

Ga Rubutun Namadi Na Neman Belin👇

“Nayi Niyyar Tsayawa a Matsayin Wanda Zai Yi Belin Wanda Ake Tuhuma(Sulaiman Aminu),Wanda Aka Bada Belin Sa,Akan Kudi Naira 3,000,000,00,Sannan Wanda Zai Tsaya Masa Zai Ajjiye 5,000,000,00,Na Yarda Zanyi Biyayya Akan Condition Din Belin Sa,Kuma Nayi Alqawari Zan Kawo Shi Kotun Duk Lokaci Zaman Kotun,Har Zuwa Qarshen Wannan Kara,Ina Fatan Kotu Mai Albarka Zata Yarsa Ta Bani Beli.

Idan Baku Manta Ba Ranar 21/05/2025 Hukumar NDLEA Ta Gabatar Da Sulaiman Dan Wawu Sanannene Dilan Kway@ A Gaban Kotu Mai Lamba 1,Qarqashin Mai Shari’a M.S Shu’aibu Akan Tuhumomi Manya Manya Har Guda 8.

Qungiyar Lauyoyi Ta Qasa Reshen Kano Ta Sanar Zata Sa Sa’ido Akan Kes Din,Amma Ga Cabinet Din Abba Yaje Yayi Belin Wannan Mutumi,Irin Wanann Kes Din Yan Siyasa,Malamai,Kai Har Wadanda Ake Ganin Qimar Su Basa Shiga Saboda Siyasarsu Da Qimar Su Zata Iya Tabuwa,Amma Gashi Shi Ya Shiga. Wannan Ya Rage Na Mai Girma Gobna.

Gaskiya Ina Shakku Anya Gobna Abba Yazo Don Ya Yaqi Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Jahar Kano? Inya Kasance Yaronsa Mai Muqamin Kwamishina Zai Yi Belin Babban Dila irin Dan Wawu,To Kode Yaje Ya Janye Daga Belin Dan Wawun,Ko Kuma a Sallame Shi,Inde Da Gaske Gobna Yake akan Masu Safarar Kwayoyi.

Ara ayinku kuna ganin gwamnan Kano abba kabir Yusuf yadace dayasaukeshi

Munasan muji raayinku ku a comment section  Allah yasa mudace
24/07/2025✍️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *