SHUGABAN ONISHA CHAMBER OF COMMERCE YARASU
•Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Anambra ta Bude Sabon Bincike Kan Mutuwar Okechukwu Akaneme
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Anambra ta bayyana cewa ta buɗe sabon bincike kan mutuwar tsohon shugaban Onitsha Chamber of Commerce, Okechukwu Akaneme, wanda rahotanni suka ce ya rasu sakamakon raunin da ya samu a wani samamen da Hukumar Shara ta Jihar (ASWAMA) ta gudanar tare da wasu jami’an ‘yan sanda.
Marigayin, wanda ke ɗaya daga cikin fitattun ‘yan kasuwa a Onitsha, ya samu raunin kashin baya a ranar 11 ga Oktoba, 2024, yayin da ake zargin cewa jami’an ASWAMA da ‘yan sanda sun yi amfani da karfin tuwo wajen aiwatar da matakin tilasta tsaftar muhalli. Ya ci gaba da fama da raunin har zuwa rasuwarsa a ranar 10 ga Yuli, 2025.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya fitar, rundunar ta ce tun a baya an fara bincike kan lamarin, inda aka gano cewa wasu daga cikin jami’an sun kauce wa ka’idojin aiki. Sai dai mutuwar Akaneme ta sa rundunar ta sake buɗe sabon babun binciken gaba ɗaya.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, CP Ikioye Orutugu, ya umurci Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da su gaggauta duba fayil ɗin lamarin domin gano gaskiya. Ya kuma tabbatar da cewa duk jami’in da aka samu da laifi ba zai tsira a hukunci ba.
Rundunar ta bayyana cewa tana cigaba da haɗa kai da sauran hukumomin gwamnati wajen tabbatar da gaskiya da adalci, tana mai jaddada aniyar ta na kare hakkin ɗan Adam da tabbatar da doka a fadin Jihar.
Wannan mutuwar ta girgiza Al’umma jahar Anambra dama yan,kasuwar jahar da ma aikatan gwamnatin inda iyalan mamachin suka bukachi tabbatar musu da anyimusu adalchi
Nantake kwamishinan jahar yabada umarnin wajan antabbatar dayin bincike mai zurfi akan mamachin
Idan ajali yai kira koba chiho sai antafi Allah yasa mudache