Jami,en Dss sunkama wani matashi dan tiktok a Jahar Kano wanda ya yada hoton shugaban kasa akwanche a gadon a sibiti bachi shugaban kasa lafiyarsa qalau
Kotu ta tura wani matashi gidan yari bisa zargin yaɗa jita-jitar mutuwar Tinubu a TikTok
Wata Babbar Kotun Majistare da ke Abuja a jiya Juma’a ta bayar da umarnin a tsare wani mashahurin mai amfani da kafafen sada zumunta, Ghali Isma’il, a Gidan Gyaran Hali na Keffi saboda yada karya cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya mutu bayan fama da wata mummunar rashin lafiya.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewa jami’an ƴansandan farin-kaya (DSS) ne su ka kama Ghali Isma’il, wanda ya wallafa wannan ikirari a TikTok mai suna @bola_asiwaju, bayan bazuwar faifen bidiyon.
Daga bisani sai SSS ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhume-tuhume biyu da suka shafi yada ƙarya da kuma tunzura jama’a da ƙiyayya ga gwamnati.
Tuhuma ta Ɗaya – Yada Labarin Ƙarya da Nufi Tayar da Hankalin Jama’a:
Bayan sauraron hujjoji daga bangaren masu kara da lauyoyin kare wanda ake tuhuma, alkalin da ke jagorantar shari’ar, Ekpeyong Inyang, ya ƙi bayar da beli, ya kuma bayar da umarnin a cigaba da tsare Ghali Isma’il. Wanda akafi sani da sultan
An dage shari’ar zuwa 19 ga Agusta.
Domin chigaba da sauraran karar tun a satin da yawuchi jami’an DSS sukaje hargida suka kamashi domin tuhumarsa da laifin fatanchi ga shugaban kasa dakuma kazafi da chin zarafinsa shugaban kasa
Fatanmu Allah yasa shugaban kasa yatausaya masa daya yafemai domin yadawo yachigaba dazama achikin iyalinsa
Allah sa mudache