Masu binchike kan belin da kwamishinan sufuri na jahar kano ya kammal binchike a kan kwamishinan

SHUGABAN KWAMITIN BINCHIKE  AKAN KWAMISHINAN SUFURI NA JAHAR KANO YA KAMMALA AIKINSA

Barrista Aminu Hussain yamikawa sakatare Jahar Kano kundin binciken ayau litinin da mai girma gwamna ya nadashi dan binchiken belin kasurgumin mai safarar kwaya wanda aka sani da dan wawu

Kwamitin da gwamnatin jihar Kano ta kafa domin binciken zargin kwamishinan sufurin jihar Ibrahim Namadi da hannu a belin mutumin da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar ya miƙa wa gwamnati rahotonsa.

A yau Litinin ne kwamitin ƙarƙashin jagorancin Barrister Aminu Hussaini ya miƙa rahoton binciken nasa ga sakataren gwamnatin jihar, Umar Farouk Ibrahim.

Barista Hussain ya ce kwamitin ya gudanar da bincike mai zurfi kuma na tsakani da Allah, ta hanyar tuntubar wadanda abin da ya shafa.

Ya kuma ce kwamitin ya gana da ma’aikatun fannin Shari’a da hukumomin tsaro da su ka haɗa da SSS, NDLEA da sauran su.

A makon da ya gabata ne dai gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin, bayan da aka zargi Namadi da ƙarbar belin Danwawu, mutumin da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi.

Batun ya janyo zazzafar muhawara a ciki da wajen jihar, inda wasu ke ganin bai kamata mutum mai matsayi irin na kwamishina ya karɓi belin mutumin da ake zargi da taimakawa wajen assasa ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar.

Lamarin da ya sa wasu ke ta kiraye-kirayen sauke shi daga muƙaminsa.

Wasu kuma sunaganin bawani abubane dan kwamishinan ya karbi belin wanda yake gaban koto tunda haryan koto bata tabbatar da shi amatsayi mailefiba tunda haryanzu kotu na chigaba da saurarar karar a gaban ta

Aljazirahausa.com.ng  tana fata Allah yabaiyan gaskiya a gurbinta.

SHIN MENENE RA AYINKU MUHADU DAKU A COMENT SECTION

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *