: Yadda Aka Kashe Bilyoyin Kudade A Zamfara A Zaben Cike Gurbi Don Ganin An Karbe Kujera Daga Jam’iyya Mai Ci A Jihar, A Daidai Lokacin Da Jihar Ke Cigaba Da Fama Da Matsalar Tsaŕo
Daga Nasiru Aminu, Gusau
Duk da irin barazanar da jihar Zamfara ke fuskanta kan matsalolin tsaro, wasu jiga-jigan ‘yan jam’iyyar adawa a jihar sun fitar da bilyoyin kudade don ganin sun samu nasara a yayin zaben cike gurbin da aka gudanar a jihar.
Rahotanni sun nuna cewa yin hakan ya fusata wasu ‘yan jihar inda suke ganin ya kamata a ce an yi amfani da wadannan kudade wajen tallafawa harkar tsaron jihar.
An rawaito cewa Gwamna Dauda Lawal Dare na iya kokarin sa wajen magance matsalar tsaro, amma maimakon irin wadannan ‘yan siyasar su mara masa baya don ganin yadda za a magance matsalar ta tsaro, amma sun ja baya saboda ba jami’iyyar su daya ba. Sun manta cewa dukkansu sun fito ne daga jihar, sanann ba su da inda ya wuce jihar.
Wata majiya ta ce, akwai jigon siyasar jihar wanda ya kashe kusan bilyan hudu don kawai ya ga jam’iyyar su ta yi nasara a zaben cike gurbin na dan majalisar jiha. Wanda hakan ya nuna karara cewa ana siyasantar da harkar tsaron jihar ta Zamfara ne.
Daga cikin wadanda ake zargi da kashe wadannan makuden kudaden don ganin jam’iyyar su ta kawo kujerar dan majalisar, har da wasu tsoffin gwamnonin jihar, wadanda kuma masu fada a ji ne a jihar, amma ake zargin sun fifita siyasa fiye da matsalar tsaro da jihar ke ciki.
Wasu masu sharhi sun bayyana cewa wadannan makuden kudaden da a ce gudummawa suka bayar don magance matsalar tsaron da jihar ke fuskanta, ya fi sakawa a harkar zaben da suka yi.
Haka kuma rahotanni sun nuna cewa an yi afmani da jami’an tsaro wajen ganin jam’iyyar adawa ta yi nasara a zaben cike gurbin, inda aka kwaso jami’an tsaron daga sassa irin su Abuja, Kaduna, Zaria, Sokoto da sauransu.
A karahe dai an shawarci wadannan ‘yan hamayyar siyasar da su mayar da wukaken su zo su marawa Gwamna Dauda Lawan Dare baya wajen ganin an shawo kan matsalar tsaro a jihar ta Zamfara, kafin daga bisani kowannensu ya sake jan daga don cigaba da siyasa.
Wani abin mamaki kuma shine, a yanzu haka karamin ministan tsaro dan jihar Zamfara, ga kuma manyan masu fada a ji dake jihar wadanda ya kamata a ce sun fifita damuwar matsalar tsaron jihar fiye da sha’anin siyasa.
Sannan ya kamata Malamai masu kishin yankin Arewa su saka baki domin ganin an fifita tsaro akan siyasa.
A jahar zamfara dama jahoyin da ake matsalar tsaro a Najeriya baki daya
Allah yasa mudace amen