Manchester United nasan sada dan wasan gaban ta aljandro ganacho ga kungiyar Chelsea

Chelsea ta matsa kaimi wajan daukar Dana wasan Manchester United ganacho

Newcastle na shirin sake tattaunawa da Liverpool kan Isak, Man U na son ta sayar da Hojlund, Wolves na son ci gaba da rike Jorgen Strand Larsen, Everton na son Ake, United na son Tottenham ta shiga zawarcin Garnacho, har yanzu Roma bata dai-dai ta da Sancho ba, har yanzu Betis na son Anthony, Spurs na son Nkuku da Akliouche, Forest na son Cash, West Ham ta bada aron Alvarez sannan tana neman yan wasa Uku, Palace Zata doke Everton a zawarcin Dibling, Dortmund Zata dau Fabio Silva, Inter na son Diouf , Rodrygo ya hakura da Madrid

Newcastle za ta sake tattaunawa da Liverpool wadda ke yukurin daukar ɗan wasanta na gaba kuma ɗan kasar Sweden Alexander Isak mai shekara 25 kan kudi fan miliyan 120 zuwa 130 .(Teamtalk)

Wolves na kokarin ganin cewa ɗan wasan gaban ta ɗan kasar Norway Jorgen Strand Larsen bai bar kungiyar ba yayin da Newcastle ta kara kaimi don siyansa kan fan miliyan 60. (Express and Star)

Manchester United ta sanar da Napoli cewa a shirye take ta ba ta lamuni tare da zabi ko wajibcin siyan ɗan wasanta ɗa=an kasar Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 22. (Fabrizio Romano)

Everton na son ta dauko ɗan wasa bayan Manchester City da Netherlands Nathan Ake mai shekara 30, domin karfafa ‘yan wasan bayan kungiyar. (Mail)

Manchester United na fatan Tottenham za ta shiga jerin kungiyoyin kwallon kafa da ke sha’awar ɗan mai kai hari ɗan kasar Argentina Alejandro Garnacho mai shekara 21, domin su fafata da Chelsea. (Givemesport)

Fatan Roma na siyan ɗan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 25, daga Manchester United na iya dogara ne kan ko wakilinsa zai rage kudin Yuro miliyan 10 da ya nema a matsayin kwamishon kafin su kulla yarjejeniya(Corriere della Sport in Italian)

Real Betis na fatan siyan ɗan wasan gaban Manchester United da Brazil Antony,mai shekara 25, sai dai ta nemi kungiyarsa ta yanke shawara kan makomarsa . (Mail)

Tottenham na zawarcin ɗan wasan tsakiya na Faransa Maghnes Akliouche, mai shekara 23, da ke taka leda a Monaco da kuma dan wasan Como da Argentina Nico Paz mai shekara 20. (Telegraph – subscription required)

Spurs na duba yiwuwar siyan dan wasan gaban Faransa Christopher Nkunku, mai shekara 27, daga Chelsea. (Teamtalk)

Nottingham Forest ta tuntubi Aston Villa kan dawo da ɗan wasan bayan Poland Matty Cash, mai shekara 28, cikin kungiyar kuma sun yi wa Sevilla tayin siyan dan wasan bayanta,Jose Angel Carmona mai shekara 23. (Mail)

West Ham ta amince ta bada aron ɗan wasanta kuma ɗan kasar Mexico Edson Alvarez mai shekara 27, ga Fenerbahce kuma suna zawarcin Dan wasan Werder Bremen da dan wasan tsakiya na kasar Austria Romano Schmid, mai shekara 25, kuma suna son dan wasan tsakiya na Lens kuma dan kasar Faransa French Andy Diouf mai shekara 22. (Guardian)

Sai dai, Inter Milan na da kwarin gwiwa cewa za ta kulla yarjejeniya shekara biyar da Diouf kan kudi kusan yuro miliyan 25 (La Gazzetta dello Sport in Italian)

Crystal Palace na kokarin ganin ta yi wa Everton pintikau a rige-rigen siyan ɗan wasan Southampton Tyler Dibling mai shekara 19, ta hanyar yi masa tayin fam miliyan 35 . (Givemesport)

Borussia Dortmund na sa ran kamala cinikin siyan ɗan wasan gaban Wolves da Portugal Fabio Silva, mai shekara 23, (Bild in German)

Rodrygo ya yarda cewa bashi da makoma karkashin Xabi Alonso kuma ya bukaci shugaban Real Madrid Florentino Pérez ya sayar da shi a wannan bazarar. (Fichajes)

Wanna Dan wasa ya kamata kungiyar ku ta dauka?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *