Rundunar yan,sanda kano tana neman matasan yan seyasar kano wanda akafi sani da dan baban gawuna da kilishi

Da dumi’dumi: rundunar ‘yan sandan Nageriya na neman matasa biyu ɗan baban Gawuna da kilishi.

Rundunar ‘yan sanda ta ƙasa ta gayyaci wasu matasa biyu daga Kano domin gabatar da su a gaban sashen musamman na bincike (FID Special Tactical Squad, Abuja) don amsa tambayoyi kan wani rahoton da aka kai ga babban sifeton ‘yan sanda na ƙasa.

Wannan na ƙunshe ne cikin wasiƙar da aka aikewa Junaidu Aminu (wanda aka fi sani da Kilishi) daga Charanchi, Kano, da kuma Tasiru Auwalu Musa wanda aka fi sani da (Ɗan Baban Gawuna) daga Hotoro Kudu Road, Kano.

A wasiƙun da aka fitar ranar 21 ga watan Agusta, 2025, an umurce su da su bayyana a ofishin FID STS, hedikwatar rundunar ‘yan sanda, Abuja (tsohuwar SARS Premises, Guzape, Abuja), a ranar 27 ga watan Agusta, 2025 da misalin ƙarfe 10 na safe.

Wasiƙar ta ce wannan kira ba wai hukunci ba ne, illa dai wani binciken gaskiya (fact finding exercise) ne da ake gudanarwa bisa doka, domin tabbatar da adalci da gaskiya a bisa tanadin Sashe na 53 (2)(c) na dokar gudanar da shari’ar laifuka ta shekarar 2015 (Administration of Criminal Justice Act 2015).

Wannan wasiƙar ta fito ne daga hannun DCP Dauda Iliya Ayuba, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda, FID Special Tactical Squad, Hedikwatar ‘Yan sanda Abuja.

Duk dai wasikar bata fito ƙarara ta bayyana dalilin gayyatar matasan ba amma rahotanni sun bayyana cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi NA ll ne ya kai korafin matasan kan zargin cin fuska a kafafen Sada zumuntar Zamani.

  1. A yau ne matasan Yakamata su gurfanar a gaban sashen binciken amma sun bayar da uzurin basu a gari sun yi tafiya kamar yadda ɗan Baban Gawuna Ya shedawa
  2. Amma basu fadin ranar da zasu dawoba inda rundunar ta tabbatar da zasu chigaba da naimansu
  3. Allah yasa mudace amen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *