- Rundunar Ƴan Sanda sun Sasanta Rikicin da ke Tsakanin Asibitin Aminu Kano da Hukumar Rarraba Hasken Wutar Lantarki ta Kano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta shiga tsakani a rikicin da ke tsakanin Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO), lamarin da ya kai ga katse wuta a asibitin, abin da ya yi barazana ga rayukan marasa lafiya.
Wannan mataki ya biyo bayan taron gaggawa da aka gudanar a ofishin Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, inda shugabannin biyu suka halarta. Shugaban asibitin, Farfesa A. Abba Sheshe, da kuma Shugaba/Manajan Darakta na KEDCO, Dakta Abubakar Shuaibu Jimeta, sun tattauna kan hanyoyin warware matsalar cikin lumana.
Bayan tattaunawa kamfanin KEDCO ya amince da gaggauta dawo da wutar lantarki a asibitin yayin zaman, domin tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan lafiya da ke da matuƙar muhimmanci ga al’umma.
Shugabannin AKTH da KEDCO sun gode wa Kwamishinan ’Yan Sanda bisa wannan shiga tsakani, tare da bayyana aniyar su ta ci gaba da yin aiki tare wajen guje wa irin wannan rikici a gaba.
Rundunar ’Yan Sanda ta bayyana wannan nasara a matsayin hujja ta jajircewarta wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma tabbatar da cewa muhimman cibiyoyi kamar asibitoci ba su fuskantar cikas a ayyukansu.
Kuma hukumar rarraba hutar lantarki tayi alkawarin chigaba da rarraba huta achiki asibitin dan kulawa da marasa lafiya dama Al,umma gabadaya Allah yasa mudace amen
Aljazirahausa.com.ng