Gwamnatin Tarayya Najeriya zata rabawa talakawa billion 330

Shirin tallafin kuɗi: Gwamnatin Tarayya ta raba Naira Biliyan 330 ga magidanta 8.1 a Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ta raba jimillar Naira biliyan 330 ga magidanta miliyan 8.1 a fadin Najeriya a karkashin shirin tallafin kuɗi (National Social Safety Net Programme), wanda aka kirkiro domin rage wa marasa galihu radadin sauye-sauyen tattalin arzikin kasar.

Ministan Kudi kuma Ministan Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun, ne ya bayyana hakan a jiya Laraba a Abuja, bayan wata ganawa da Kwamitin Musamman na Shugaban Kasa kan Zuba Daukar nauyin Jin Kai, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa a watan Fabrairu.

Edun ya bayyana cewa shirin, wanda ya fuskanci jinkiri a farkon shekara, yanzu ya dawo sakamakon la’akari da nasarar da aka samu na shigar da bayanan Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN) ga waɗanda za su ci gajiyar shirin.

Ya ce wannan hadakar bayanan ta taimaka matuka wurin tabbatar da gaskiya da rufe hanyoyin zamba, da kuma kawarda katsalandan na siyasa a cikin shirin.

A cewar Ministan, daga cikin gidaje miliyan 19.7 da aka tantance a cikin rajistar jin kai ta kasa (National Social Register) — wanda ke wakiltar kimanin ƴan Najeriya miliyan 70, gidaje miliyan 8.1 sun riga sun samu akalla sashe daya na tallafin Naira 25,000.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin sun samu sau biyu zuwa uku, dangane da sakamakon tantancewar da aka gudanar.

Ya kuma kara da cewa gidaje miliyan 2.2 sun samu kudin a zagaye na baya-bayan nan, bayan da aka tabbatar da lambar BVN da NIN dinsu.

Edun ya danganta jinkirin da aka samu da rashin cika shirin rijistar NIN, amma ya jaddada cewa duk wasu kudaden da suka rage za a kammala rabawa kafin karshen shekarar 2025.

Sai kuyi sauri ku chike takardun nema  dan kowa yasamu Allah yasa mudache

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *