BABBAN MINISTAN TSARO BADARU TALAMIS YAYI MURABUS DAGA MUKAMINSA
Janar Christopher Musa zai maye gurbin Badaru a matsayin Ministan Tsaro
Idan ba a samu wani sauyi na ƙarshe ba, Shugaba Bola Tinubu zai naɗa tsohon Babban Hafsan Tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa, domin ya maye gurbin Badaru Abubakar a matsayin ministan tsaro.
Badaru Abubakar ya yi murabus daga mukaminsa na ministan tsaro a ranar Litinin, inda ya danganta hakan da dalilai na lafiya.
Majiyoyi masu tushe da suka san da lamarin sun shaida wa wakilinmu cewa Shugaba Tinubu ya kammala shirye-shiryen naɗa Mista Musa domin ya maye gurbin Badaru Abubakar, bayan matsin lamba daga cikin gida na ganin an saka tsohon jami’in soja a majalisar zartarwarsa.
DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa tsohon babban hafsan tsaron ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa a daren Litinin.
Wakilin jaridar The Punch ya ga Mista Musa yana isa Fadar Ƙasa da ƙarfe 7:03 na yamma a ranar Litinin, inda wani babban jami’in tsaro ya jagorance shi zuwa ofishin Shugaban Ƙasa.inda duk wasu shirye-shiryen na maye gurbin ministan tsaro yadau salo inda akesaran maye gurbin sa da musa
A gefe guda daya
Anyi nasarar kama yan Bindiga mutun hudu a jahar kano inda aka kamasu awata tashar mota dake kofar ruwa inda sukai kokarin guduwa da taimakon Al,umma da jami’an tsaro tunudai jami’an tsoro sukai gaba dasu
Allah ubangiji kabamu zaman lafiya da kwanchiyar hankali mai dorewa Akasarmu dama jahar mu Amen