JUYIN MULKIN BENIN YA BAR BAYA DA KURA SOJOJIN BENIN π§π― SUNYI JUYIN MULKI
Kwana biyu an wayi gari da labarin juyin mulkin Sojoji a Kasar Benin dake makwabta da Nigeria ta jihar Lagos
Daga bisani Gwamnatin Nigeria ta tura jiragen yaki domin su dakile juyin mulkin, maganganu biyu sun kasu, (1) Gwamnatin Benin da na Nigeria sunce juyin mulkin baiyi nasara ba, (2) wani rahoton kuma na cewa har zuwa yanzu Sojojin Benin suna rike da mulkin
A yau Maigirma Shugaban Nigeria ya nemi amincewar Majalisar Dattawan Nigeria domin a tura mayakan Sojojin Nigeria zuwa Kasar Benin, kuma Majalisar Dattawa ta amince, masa to kunga akwai alamun dai har yanzu Sojojin Benin suna rike da mulki, za’a tura Sojojin Nigeria su koresu daga mulki kenan? Imba haka ba ai babu amfanin tura Sojojin tunda ance juyin mulkin baiyi nasara ba
Ana haka kuma sai ga wani labari cewa Kasar Burkina Faso ta rike wasu Sojojin saman Nigeria da suka sauka a jirgi ba bisa ka’ida ba, kamar yadda sanarwa daga Mahukuntan Kasar Burkina Faso ya fito, ita kuma rundinar Sojin saman Nigeria tace Sojojin sun sauka a Kasar Burkina Faso bisa ka’ida, a halin yanzu dai Sojojin suna tsare a can Kasar, mataki na gaba shine ko dai Burkina Faso ta sako Sojojin Nigeria da jirgin ko kuma a tura dakaru kenan su kubutar da su?
A daidai lokacin kuma Kasashen Niger, Burkina Faso da Mali sukayi kakkausan gargadi wa Nigeria cewa idan wani jirgin Nigeria ya sake keta sararin samaniyarsu ba tare da izni ba zasu kakkabo shi, saboda sun ji zafin yadda jirgin Nigeria ya kai agajin gaggawa zuwa Benin kenan, hakan na nufin danganta ta kara dagulewa kenan
Kun ga faruwar wadannan ina jiye mana tsoron abubuwan da zasu biyo baya, zaman dardar tsakanin Kasarmu Nigeria da wadancan Kasashe renon Faransa na kara yin kamari, a lokacin da Faransa take cewa zata hada kai da Nigeria domin a yaki matsalar tsaro
Kasashen Burkina Faso, Mali da Niger duka Sojoji ne ke mulkinsu kuma renon Faransa ne wanda a halin yanzu Kasar Russia ce Uwargijiyarsa, wannan yasa Faransa bata da wani zabi a Kasashen sahel face ta kama Kasarmu Nigeria ta hanyar hadin kai
Lamarin yana bukatar taka tsantsan sosai, shiga yaki da Kasashen ba zai haifar da komai ba sai koma baya, bama son yaki, gara a warware matsalar ta hanyar diplomasiyya shi yafi alheri
Muna rokon Allah Ya bamu zaman lafiya a Nahiyar mu na Afirka da duniya baki daya
Ya ubangiji karusa duk wani maisan yatada rigima
Allah kabamu lafiya da zaman lafiyarΒ amen