Sojoji sun kama kasurgumin dan boko haram zai tashi bomb

YANZU-YANZU: Rundunar Sojin Najeriya Ta Kama ’Dan Kunar Baƙin Wake Masu Shirin Tada Bam a Borno.

Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa Maso Gabas (JTF NE), Operation Hadin Kai (OPHK), ta samu gagarumar nasara a yaƙin da take yi da ta’addanci, bayan kama wani da ake zargin babban dan kunar baƙin wake tare da kwace kayayyakin hada bam (IED) a Jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa kamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da kuma ci gaba da ayyukan haɗin gwiwa da dakarun Bataliya ta 152 Task Force suka gudanar tare da sauran hukumomin tsaro, domin tabbatar da tsaro a garin Banki da ke Ƙaramar Hukumar Bama.

Da misalin ƙarfe 5:40 na yammacin ranar Litinin, 29 ga Disamba, 2025, jami’an tsaro da aka girke a Babban Masallacin Banki sun kama wani da ake zargin dan kunar baƙin wake mai suna Abubakar Mustapha, yayin da yake dauke da shirye-shiryen kayan bam (IED), abin da ke nuna yana dab da aiwatar da harin ta’addanci.

Binciken farko ya tabbatar da cewa wanda ake zargin dan asalin Ƙaramar Hukumar Bama ne, kuma an same shi da wasu karin kayayyaki masu alaka da ayyukan ta’addanci. A halin yanzu yana tsare domin zurfafa bincike, don gano masu daukar nauyinsa da sauran abokan aikinsa a kungiyoyin ta’adda.

A wani bangare na wannan nasara, dakarun soji da ke bakin iyakar Najeriya da Kamaru sun tare wata mota kirar Peugeot dauke da buhuna shida na takin urea, wani muhimmin sinadari da ake amfani da shi wajen hada bama-baman IED. An kwace motar da takin tare da cafke wadanda lamarin ya shafa.

Ci gaba da binciken bayanan sirri daga wannan kamen ya kai ga cafke dillalin takin, tare da kwato wasu karin buhuna shida, lamarin da ya kawo adadin takin urea da aka kwace zuwa buhuna goma sha biyu (12) gaba ɗaya.

  • Dakarun Operation Hadin Kai na ci gaba da mamaye yankunan da ke karkashin alhakin su ta hanyar sintiri mai tsauri da ayyukan da ke bisa bayanan sirri, domin hana ’yan ta’addan JAS/ISWAP damar aikata hare-hare da kuma kare rayuka da dukiyoyin fararen hula.
  • Allah kakawowa Najeriya sauki da afuwa kan yan ta adda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *